Don me ka yi annabci da sunan Ubangiji, ka ce wannan Haikali zai zama kamar Shilo, wannan birni kuma zai zama kufai, ba mazauna a ciki?” Sai jama'a duk suka taru, suka kewaye Irmiya cikin Haikalin Ubangiji.
“Ni Ubangiji Mai Runduna Allah na Isra'ila, na ce, ku da kanku kun ga masifar da na aukar wa Urushalima, da dukan garuruwan Yahuza. Yanzu sun zama kufai, ba wanda yake zaune a cikinsu,
Zan yi kuka in yi kururuwa saboda tsaunuka, Zan yi kuka saboda wuraren kiwo, Domin sun bushe sun zama marasa amfani. Ba wanda yake bi ta cikinsu. Ba a kuma jin kukan shanu, Tsuntsaye da namomin jeji, sun gudu sun tafi.