Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 5:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Saboda wannan zuciyarmu ta ɓaci, Idanunmu kuma suka duhunta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Domin wannan zuciyarmu ta yi sanyi; domin waɗannan abubuwa idanunmu sun dushe

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 5:17
17 Iomraidhean Croise  

Baƙin cikina ya kusa makantar da ni, Hannuwana da ƙafafuna sun rame, sun zama kamar kyauro.


Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, Gama ina shan wahala, Idanuna sun gaji saboda yawan kuka, Na kuwa tafke ƙwarai!


An ragargaza ni sarai, an kuwa ci nasara a kaina, Na damu a zuciyata, ina nishi don zafi.


Idanuna sun yi kumburi saboda yawan kuka, Har da ƙyar nake iya gani, Duk kuwa saboda abokan gābana!


Na gaji da kira, ina neman taimako, Maƙogwarona yana yi mini ciwo, Idanuna duka sun gaji, Saboda ina zuba ido ga taimakonka.


Me ya sa kuke ta tayarwa? Kuna so a ƙara muku hukunci ne? Ya Isra'ila, kanki duka rauni ne, zuciyarki da kwanyarki suna ciwo.


Muryata ƙarama ce, ba kuma ƙarfi, Na kuwa yi kuka kamar kurciya, Idanuna sun gaji saboda duban sama. Ya Ubangiji, ka cece ni daga dukan wannan wahala.


Ubangiji ya yi tambaya ya ce, “Me nake gani? Sun tsorata, suna ja da baya, An ci sojojinsu, suna gudu, Ba su waiwayen baya, akwai tsoro a kowane sashi.”


Baƙin cikina ya fi ƙarfin warkewa, Zuciyata ta ɓaci ƙwarai!


“Daga sama ya aukar da wuta a cikin ƙasusuwana. Ya kuma kafa wa ƙafafuna ashibta, Ya komar da ni baya, Ya bar ni a yashe, sumamme dukan yini.


“Ka sa mugayen ayyukansu su bayyana a gabanka, Sa'an nan ka hukunta su kamar yadda ka hukunta ni saboda dukan laifofina. Gama nishe-nishena sun yi yawa. Zuciyata kuma ta karai.”


Idanuna sun dushe saboda kuka, Raina yana cikin damuwa. Zuciyata ta karai saboda halakar mutanena, Gama 'yan yara da masu shan mama Sun suma a titunan birnin.


Zai sa zukatansu su narke, da yawa kuma su fāɗi a ƙofofinsu. Na ba da takobi mai walƙiya. An yi shi kamar walƙiya, an wasa shi don kashe-kashe.


Idan sun tambaye ka, ‘Me ya sa kake nishi?’ Sai ka ce musu, ‘Saboda labarin abin da yake zuwa. Sa'ad da ya zo, kowace zuciya za ta narke, hannuwa duka za su yi suwu, kowane ruhu kuma zai suma, gwiwoyi duka kuwa za su rasa ƙarfi kamar ruwa. Ga shi, abin yana zuwa, zai tabbata,’ ni Ubangiji Allah na faɗa.”


“Amma ga waɗanda suka ragu, zan sa fargaba a zuciyarsu sa'ad da suke a ƙasar maƙiyansu. Ko motsin ganye kawai ma zai razanar da su su sheƙa a guje kamar waɗanda ake fafara da takobi, ga shi kuwa, ba mai korarsu, za su kuwa fāɗi.


Domin haka zan buge ku da ciwo, In maishe ku kufai saboda zunubanka.


Ba za ku sami zaman lafiya wurin waɗannan al'ummai ba, ko tafin ƙafarku ma ba zai sami wurin hutawa ba. Ubangiji kuma zai sa fargaba a zuciyarku, ya sa idanunku su lalace, ranku zai yi suwu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan