Hakika Urushalima ta shiga uku! Yahuza tana kan fāɗuwa! Duk abin da suke faɗa, da abin da suke yi, na gāba da Ubangiji ne, a fili suke raina Allah, shi kansa.
Ubangiji ya ce wa Irmiya, “Ka faɗa wa sarki da sarauniya, uwarsa, su sauka daga gadon sarautarsu, Domin an tuɓe kyakkyawan rawanin sarautarsu daga kansu.
Muguntarka za ta hore ka, Riddarka kuma za ta hukunta ka. Sa'an nan za ka sani, ka kuma gane, Ashe, mugun abu ne, mai ɗaci, a gare ka Ka rabu da Ubangiji Allahnka, Ba ka tsorona a zuciyarka. Ni Ubangiji, Allah Mai Runduna na faɗa.”
Amma sa'ad da suka shiga cikinta suka mallake ta, ba su yi biyayya da muryarka ba, ba su kiyaye dokokinka ba, ba su aikata dukan abin da ka umarce su ba, saboda haka ka sa wannan masifa ta auko musu.
Urushalima wadda take cike da mutane a dā, Yanzu tana zaman kaɗaici! Tana zama kamar mace wadda mijinta ya rasu, Ita wadda dā ta zama babba a cikin sauran al'ummai! Ita wadda take a dā sarauniya a cikin larduna, Ta zama mai biyan gandu!
“Ka duba, ya Ubangiji, ina shan wahala, Raina yana cikin damuwa, Zuciyata tana makyarkyata saboda tayarwata. A titi takobi yana karkashewa, A gida kuma ga mutuwa.
Urushalima ta yi zunubi ƙwarai da gaske, Saboda haka ta ƙazantu, Dukan waɗanda suka girmama ta sun raina ta Domin sun ga tsiraicinta, Ita kanta ma tana nishi, ta ba da baya.
Ubangiji ya duhunta Sihiyona saboda fushinsa! Daga Sama kuma ya jefar da darajar Isra'ila a ƙasa. Bai kuma tuna da matashin sawayensa ba A ranar fushinsa.
Ni Ubangiji Allah na ce, ka cire rawaninka, ka ɗauke kambinka. Abubuwa ba za su kasance kamar yadda suke a dā ba. Za a ɗaukaka ƙasƙantacce, amma a ƙasƙantar da maigirma.
Kada ka ji tsoron wuyar da za ka sha. Ga shi, Iblis yana shiri ya jefa waɗansunku a kurkuku don a gwada ku, za ku kuwa sha tsanani har kwana goma. Ka riƙi amana ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka kambin rai.
Isra'ilawa fa suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa, suka zuba a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a ranan nan, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi.” Sama'ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra'ilawa.