15 Farin cikinmu ya ƙare, Raye-rayenmu sun zama makoki.
15 Farin ciki ya rabu da zuciyarmu; rayuwarmu ta zama makoki.
Saboda haka garayata ta zama ta makoki, Sarewata kuma ta zama muryar masu kuka.”
Ka mai da baƙin cikina Ya zama rawar farin ciki, Ka tuɓe mini tufafin makoki, Ka sa mini na farin ciki.
Banda haka zan kawar da muryar sowa da ta farin ciki, da ta ango da ta amarya, da amon dutsen niƙa daga gare su. Zan kashe hasken fitilunsu.
Zan mai da bukukuwanku makoki, In sa waƙoƙinku na murna su zama na makoki. Zan sa muku tufafin makoki, In sa ku aske kanku. Za ku yi makoki kamar iyayen da suka rasa tilon ɗansu. Ranan nan mai ɗaci ce har ƙarshe.