Gama ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, zan sa muryar murna, da ta farin ciki, da ta ango, da ta amarya, su ƙare a wurin nan a idonka da zamaninka.
Hanyoyin Sihiyona suna baƙin ciki Domin ba mai halartar ƙayyadaddun idodi. Dukan ƙofofinta sun zama kufai, Firistocinta suna nishi, Budurwanta kuma suna wahala, Ita kanta ma tana shan wuya ƙwarai.
Zan hukunta ta saboda kwanakin idodin gunkin nan Ba'al. A kwanakin nan takan ƙona musu turare, Ta yi ado da zobe da lu'ulu'ai, Ta bi samarinta, amma ta manta da ni.” In ji Ubangiji.
Ba za a ƙara jin kiɗan masu molo, da mawaƙa, da masu sarewa, da masu bushe-bushe a cikinki ba, Ba kuma za a ƙara ganin mai kowace irin sana'a a cikinki ba, Ba kuma za a ƙara jin niƙa a cikinki ba,