Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 5:13 - Littafi Mai Tsarki

13 An tilasta wa samari su yi niƙa, Yara kuma suna tagataga da kayan itace.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Samari suna faman yin niƙa; yara kuma suna fama da ƙyar da nauyin kayan itace.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 5:13
11 Iomraidhean Croise  

To, bari matata ta yi wa wani abinci, Bari waɗansu su kwana da ita.


Suka kuwa naɗa musu shugabannin aikin gandu domin su wahalshe su da mawuyacin aiki. Aka sa su su gina wa Fir'auna biranen ajiya, wato Fitom da Ramases.


Kowane ɗan farin da yake ƙasar Masar zai rasu, daga ɗan farin Fir'auna wanda zai hau gadon sarautarsa, har zuwa ɗan farin kuyanga wadda take niƙa, da dukan ɗan farin shanu.


Ana nan wata rana, sa'ad da Musa ya yi girma, ya tafi wurin mutanensa, sai ya ga yadda suke shan wahala. Ya kuma ga wani Bamasare yana dūkan Ba'ibrane, ɗaya daga cikin 'yan'uwansa.


Idan wani ya ga kaya ya danne jakin maƙiyinsa kada ya tafi ya bar shi da shi, sai ya taimaka a ɗaga masa.


Ki juya dutsen niƙa, ki niƙa gari! Ki kware lulluɓi! Ki tuɓe kyawawan tufafinki!


“To, ba irin wannan azumi ne na zaɓa ba? Wato ku kwance sarƙoƙin mugunta, ku kwance masu karkiya, ku 'yantar da waɗanda ake zalunta, ku kakkarye kowace karkiya.


Yara sukan tara itace, iyaye maza sukan haɗa wuta, iyaye mata sukan kwaɓa ƙullu don su yi wa gunkin nan wadda ake kira sarauniyar sama, waina. Sukan kuma miƙa wa gumaka hadayu na sha domin su tsokane ni.”


Sukan ɗaura kaya masu nauyi, masu wuyar ɗauka, su jibga wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu ko tallafa musu da ɗan yatsa ba sa yi.


Filistiyawa fa suka kama shi, suka ƙwaƙule idanunsa, suka gangara da shi zuwa Gaza. Suka ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla. Ya yi ta niƙa a kurkuku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan