Na yi fushi da mutanena, Na maishe su kamar su ba nawa ba ne. Na sa su a ƙarƙashin ikonki, Ba ki kuwa yi musu jinƙai ba, Har da tsofaffi ma kin ba su wuya.
Ya Ubangiji, ka duba, ka gani! Wane ne ka yi wa haka? Mata za su cinye 'ya'yansu da suke reno? Ko kuwa za a kashe firist da annabi A cikin Haikalin Ubangiji?