Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 5:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Ya Ubangiji, ka tuna da abin da ya same mu. Ka duba, ka ga yadda muka zama abin kunya!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Ka tuna, ya Ubangiji, abin da ya faru da mu; duba, ka ga kunyar da muka sha.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 5:1
26 Iomraidhean Croise  

Sai suka ce mini, “Waɗanda suka tsira, suka koma daga zaman talala, da suke can lardin, suna cikin wahala ƙwarai, suna kuma shan kunya. Garun Urushalima kuma ya rushe, ƙofofi sun ƙone.”


Ka tuna da maganar da ka umarci bawanka Musa cewa, ‘Idan kun yi rashin aminci, zan warwatsa ku cikin al'ummai.


Sai ni, Nehemiya, na yi addu'a, na ce, “Ka ji, ya Allahnmu, gama ana raina mu, ka sa ba'arsu ta koma kansu, ka sa a washe su a kai su ƙasar bauta.


Ka tuna, ya Allah, kai ka halicce ni, da yumɓu kuwa ka yi ni. Za ka murtsuke ni ne, in kuma koma ƙura?


“Ka tuna, ya Ubangiji, raina iska ne kawai, Farin cikina ya riga ya ƙare.


Ka dubi wahalata, ka cece ni, Gama ban ƙi kulawa da dokarka ba.


Amma ka tuna fa, ya Ubangiji, abokan gābanka suna yi maka ba'a, Su wawaye ne waɗanda suke raina ka.


Ya Ubangiji, ka rama wa al'umman nan har sau bakwai, Saboda tsiwace-tsiwacen da suka yi maka.


Sauran al'ummar da take kewaye da mu, Suka maishe mu abin ba'a, suka yi mana dariya, Suka yi mana ba'a.


Ya Urushalima, na sa matsara a garukanki Ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana. Za su tuna wa Ubangiji da alkawaransa, Ba kuwa za su bari ya manta ba!


Sa'an nan Irmiya ya ce, “Ya Ubangiji, ka sani. Kai ne, ka ziyarce ni, Ka kuma sāka wa waɗanda suke tsananta mini. Ka sani saboda kai nake shan zargi.


Mun sha kunya saboda zargin da ake yi mana, Kunya ta rufe mu, Gama baƙi sun shiga tsarkakan wurare na Haikalin Ubangiji.


Dukan jama'arta suna nishi don neman abinci, Sun ba da kayansu masu daraja saboda abinci Don su rayu. “Ya Ubangiji ka duba, ka gani, Gama an raina ni.”


“Ka duba, ya Ubangiji, ina shan wahala, Raina yana cikin damuwa, Zuciyata tana makyarkyata saboda tayarwata. A titi takobi yana karkashewa, A gida kuma ga mutuwa.


Ƙazantarta tana cikin tufafinta, Ba ta tuna da ƙarshenta ba, Domin haka faɗuwarta abar tsoro ce, Ba ta da mai yi mata ta'aziyya. “Ya Ubangiji, ka dubi wahalata, Gama maƙiyi ya ɗaukaka kansa!”


Dukan masu wucewa suna yin miki tafin raini. Suna yi wa Urushalima tsāki, Suna kaɗa mata kai, suna cewa, “Ai, Urushalima ke nan, Birnin nan da ake cewa mai cikakken jamali, Wanda ya ƙayatar da dukan duniya?”


Ya Ubangiji, ka duba, ka gani! Wane ne ka yi wa haka? Mata za su cinye 'ya'yansu da suke reno? Ko kuwa za a kashe firist da annabi A cikin Haikalin Ubangiji?


Ka tuna da azabata, da galabaitata, Da ɗacin raina, da kumallon da nake fama da shi.


Har lokacin da Ubangiji daga Sama ya duba, ya gani.


“Ya Ubangiji, ka ji zargi Da dukan dabarun da suke yi mini.


Ya Ubangiji, na ji labarinka, Sai tsoro ya kama ni. Ka maimaita manyan ayyukanka a zamaninmu, Ayyukan da ka saba yi. Ka yi jinƙai ko lokacin da kake fushi.


Ya kuma ce, “Ya Yesu, ka tuna da ni, sa'ad da ka shiga sarautarka.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan