Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 4:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Yanzu fuskokinsu sun fi kukunniya baƙi, Ba a iya fisshe su a titi ba, Fatar jikinsu ta liƙe wa ƙasusuwansu, Sun bushe kamar itace.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Amma yanzu sun fi dare duhu; ba a iya gane su a tituna. Fatar jikinsu ta manne da ƙasusuwansu; sun bushe kamar itace.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 4:8
17 Iomraidhean Croise  

Fatar jikina ta saki, ba ƙarfi, Da ƙyar na kuɓuta.


Suka hango Ayuba tun daga nesa, amma ba su gane shi ba. Da suka gane shi sai suka fara kuka da murya mai ƙarfi. Suka kyakkece tufafinsu saboda baƙin ciki, suka ɗibi ƙura suka watsa a kawunansu.


Fatata ta takura, ta zama baƙa, Ƙasusuwana suna zogi saboda zafi,


Yakan rame ƙangayau, ƙasusuwansa duk a waje.


Raina kamar inuwar maraice yake, Kamar busasshiyar ciyawa nake.


Na zama marar amfani kamar salkar ruwan inabi wanda aka jefar da ita, Duk da haka ban manta da umarnanka ba.


Ka hukunta ni dare da rana, ya Ubangiji, Ƙarfina duka ya ƙare sarai, Kamar yadda laima yake bushewa, Saboda zafin bazara.


Saboda fushinka ina ciwo mai tsanani, Duk jikina ya kamu da ciwo saboda zunubina.


Mutane da yawa suka gigice sa'ad da suka gan shi, Ya munana har ya fita kamannin mutum.


Fatar jikinmu ta yi zafi kamar murhu, Saboda tsananin yunwa.


Da zuwanta mutane sukan firgita, Dukan fuskoki sukan ɓaci.


Nineba ta halaka! ta lalace, ta zama kufai! Zukata sun narke, gwiwoyi suna kaɗuwa! Kwankwaso yana ciwo, Fuskoki duka sun kwantsare!


‘Ko da ƙurar garinku da ta ɗafe a jikin ƙafafunmu ma, mun karkaɗe muku. Amma duk da haka ku sani Mulkin Allah ya kusato.’


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan