Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 4:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Keɓaɓɓunta sun fi dusar ƙanƙara tsabta, Sun kuma fi madara fari. Jikunansu sun fi murjani ja. Kyan tsarinsu yana kama da shuɗin yakutu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 ’Ya’yan sarakunansu sun fi ƙanƙara haske sun kuma fi madara fari, jikunansu sun fi murjani ja, kyansu kamar shuɗin yakutu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 4:7
15 Iomraidhean Croise  

Ko zinariyar Ofir, ko onis, Ko saffir, wato duwatsu masu daraja, ba za su iya biyan tamaninta ba.


Kada ma a ko ambaci murjani, Da duwatsu masu walƙiya. Gama tamanin hikima ya fi na lu'ulu'ai mafiya daraja duka.


Ka sa 'ya'yanmu maza waɗanda suke cikin samartaka, Su zama kamar itatuwan da yake girma da ƙarfi. Ka sa 'ya'yanmu mata Su zama kamar al'amudai, Waɗanda suke adanta kusurwoyin fāda.


Ka kawar da zunubina, zan kuwa tsarkaka, Ka wanke ni, zan kuwa fi auduga fari.


Suka ga Allah na Isra'ila. Wurin da yake ƙarƙashin tafin ƙafafunsa yana kama da daɓen da aka yi da dutsen yakutu, garau kamar sararin sama.


Ƙaunataccena kyakkyawa ne ƙaƙƙarfa kuma, Da ƙyar a sami ɗaya irinsa a cikin dubu goma.


Cinyoyinsa kamar ginshiƙan da aka yi da dutsen alabasta, Aka kafa su a cikin kwasfar zinariya. Kamanninsa kamar Dutsen Lebanon ne, Da itatuwan al'ul ɗinsa mafi kyau.


A ƙarshen kwana goma ɗin, sai aka ga fuskokinsu suna sheƙi, sun kuma yi ƙiba fiye da samarin da suke cin abinci irin na sarki.


Domin zai zama mai girma a wurin Ubangiji, Ba kuwa zai sha ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Za a cika shi da Ruhu Mai Tsarki Tun yana cikin uwa tasa.


gama za ki yi juna biyu, ki haifi ɗa. Ba za ki taɓa aske kansa ba Zai zama keɓaɓɓe ga Allah tun daga cikin ciki. Shi ne zai ceci Isra'ilawa daga hannun Filistiyawa.”


Amma ya ce mini, zan yi juna biyu, in haifi ɗa, don haka kada in sha ruwan inabi, ko abin sa maye, kada kuma in ci haramtaccen abu, gama yaron zai zama keɓaɓɓe ga Allah tun daga cikin ciki har zuwa ranar da zai rasu.”


A ƙarshe ya faɗa mata ainihin gaskiyar, ya ce mata, “Ba a taɓa aske gashin kaina ba, gama ni keɓaɓɓe ga Ubangiji ne tun daga cikin uwata. Idan aka yi mini aski, to, ƙarfina zai rabu da ni, in zama marar ƙarfi kamar kowa.”


Yesse kuwa ya aika aka taho da shi. Ga shi kuwa kyakkyawa ne, idanunsa suna sheƙi. Sai Ubangiji ya ce wa Sama'ila, “Tashi ka zuba masa man keɓewa, shi ne sarkin.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan