Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 4:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Su waɗanda suka ci abubuwa masu daɗi, Sun halaka a titi. Su waɗanda aka goye su da alharini, Yanzu suna kwance a kan tsibin toka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Waɗanda a dā sukan ci abinci mai daɗi yanzu su ne masu bara a tituna. Waɗanda a dā suke sa kaya masu kyau yanzu suna kwance a kan tarin toka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 4:5
17 Iomraidhean Croise  

“Ku 'yan matan Isra'ila, ku yi makoki domin Saul! Ya suturta ku da mulufi mai ƙayatarwa, Ya yi muku adon lu'ulu'u da zinariya.


Amma Rabshake ya ce musu, “Ai, ubangidana bai aike ni in yi wannan magana ga ubangidanku da ku kaɗai ba, amma ga dukan mutanen da suke zaune a kan garu, waɗanda aka ƙaddara su tare da ku don su ci najasarsu su sha fitsarinsu.”


Sukan jiƙe sharkaf da ruwan sama wanda yake kwararowa daga kan duwatsu. Sun takure a gefen duwatsu neman mafaka.


Ba ta jin tsoron lokacin sanyi gama 'ya'yanta duka suna da tufafi masu ƙauri.


Dukan jama'arta suna nishi don neman abinci, Sun ba da kayansu masu daraja saboda abinci Don su rayu. “Ya Ubangiji ka duba, ka gani, Gama an raina ni.”


Har ma ya so ya cika cikinsa da kwasfar da aladu suke ci, amma ba wanda ya ba shi wani abu


“An yi wani mai arziki, mai sa tufafin jan alharini da farare masu ƙawa, yana shan daularsa a kowace rana.


To, kallon me kuka je yi? Wani mai adon alharini? Ai kuwa, masu adon gaske, masu zaman annashuwa, a fāda suke.


Amma wadda take zaman annashuwa kuwa, kamar matacciya take, ko da tana a raye.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan