Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 4:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ko diloli ma sukan ba 'ya'yansu mama, Su shayar da su. Amma mutanena sun zama kamar jiminai cikin jeji.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Ko diloli suna ba ’ya’yansu nono su sha, amma mutanena sun zama marasa zuciya kamar jiminai a cikin jeji.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 4:3
14 Iomraidhean Croise  

Sa'ad da na tashi da safe don in ba ɗana mama, sai ga shi, matacce. Da na duba sosai, sai na ga ba nawa ba ne, wanda na haifa.”


A hasumiyarta da fādodinta za a ji amsar ihun koke-koken kuraye da na diloli. Lokacin Babila ya yi! Kwanakinta sun kusa ƙarewa!”


Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su tsiro su yi girma a cikin dukan fādodi da garuruwa masu garuka, diloli da mujiyoyi za su zauna a cikinsu.


Saboda haka Ubangiji ya amsa ya ce, “Mace za ta iya mantawa da jaririnta, Ta kuma ƙi ƙaunar ɗan da ta haifa? Ya yiwu mace ta manta da ɗanta, To, ni ba zan taɓa mantawa da ku ba.


Zan sa su ci naman 'ya'yansu mata da maza. Kowa zai ci naman maƙwabcinsa cikin damuwa a lokacin da za a kewaye su da yaƙi, zai sha wahala daga wurin abokan gābansa da waɗanda suke neman ransa.’


Ya Ubangiji, ka duba, ka gani! Wane ne ka yi wa haka? Mata za su cinye 'ya'yansu da suke reno? Ko kuwa za a kashe firist da annabi A cikin Haikalin Ubangiji?


Mata masu juyayi, da hannuwansu Suka ɗauki 'ya'yansu, suka dafa, Suka zama musu abinci a lokacin halakar mutanena.


Ubanni za su cinye 'ya'yansu, 'ya'ya kuma za su cinye ubanninsu. Zan hukunta ki, waɗanda kuma suka tsira zan watsar da su ko'ina.


Za ku ci naman 'ya'yanku mata da na 'ya'yanku maza.


da marasa fahimta, da masu ta da alkawari, da marasa ƙauna, da marasa tausayi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan