Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 4:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Ya Sihiyona, hukunci a kan muguntarki ya ƙare, Ba zai ƙara barinki a ƙasar bauta ba. Amma zai hukunta ki saboda muguntarki, ya Edom, Zai tone zunubanki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Ya Diyar Sihiyona, hukuncinki zai ƙare; ba zai sa zaman bautarki yă yi tsayi ba. Amma ya Diyar Edom, zai hukunta zunubinki yă tona tsiraicinki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 4:22
17 Iomraidhean Croise  

Ka tuna, ya Ubangiji, da abin da Edomawa suka yi, A ranar da aka ci Urushalima. Ka tuna da yadda suka ce, “A ragargaza ta har ƙasa!”


Ka ƙarfafa jama'ar Urushalima. Ka faɗa musu sun sha wahala, ta isa, Yanzu kuwa an gafarta musu zunubansu. Na yi musu cikakken hukunci saboda dukan zunubansu.”


Urushalima, ki ƙarfafa, ki yi girma kuma! Birni mai tsarki na Allah, Ki yafa wa kanki jamali! Arna ba za su ƙara shiga ta ƙofofinki ba.


Ba za a ƙara jin hayaniyar tashin hankali ba, Ba za a ƙara aukar wa ƙasar da ɓarna ba. Zan kiyaye ki, in kāre ki kamar garu, Za ki yi yabona domin na cece ki.


Zan yi madawwamin alkawari da su, ba zan fasa nuna musu alheri ba, zan kuwa sa tsorona a zukatansu domin kada su bar bina.


Zan kuma mayar wa mutanen Yahuza da mutanen Isra'ila da arzikinsu, in sāke kafa su kamar yadda suke a dā.


Zan shafe dukan laifin da suka yi mini, in kuma gafarta musu dukan zunubansu da tayarwar da suka yi mini.


Amma na tsiraita Isuwa sarai, Na buɗe wuraren ɓuyarsa, Har bai iya ɓoye kansa ba, An hallakar da mutanen Isuwa Tare da 'yan'uwansa da maƙwabtansa, Ba wanda ya ragu.


Ni Ubangiji na ce sa'ad da lokacin nan ya yi za a nemi laifi da zunubi a cikin Isra'ila da Yahuza, amma ba za a samu ba, gama zan gafarta wa sauran da suka ragu.


Ki yi farin ciki, ki yi murna, ke Edom, Wadda kike zaune cikin ƙasar Uz. Amma fa za a ba ki ƙoƙo ki sha, Ki bugu har ki yi tsiraici.


Gama zunubin mutanena Ya fi zunubin Saduma, Wadda Ubangiji ya hallakar da ita nan da nan.


Sa'an nan al'ummai za su sani, ni ne na tsarkake Isra'ila sa'ad da na kafa Haikalina a tsakiyarsu har abada.”


Annoba za ta kashe wanda yake nesa, wanda yake kusa kuwa takobi zai kashe shi. Yunwa kuma za ta kashe wanda yaƙi ya kewaye shi. Ta haka zan aukar da fushina a kansu.


“Saboda kama-karyar da ka yi wa Yakubu ɗan'uwanka, Za a sa ka ka sha kunya, Za a hallaka ka har abada.


Na ƙi Isuwa da zuriyarsa, na hallaka ƙasarsa ta kan tudu, wurin zamansa kuwa na ba namomin jeji.”


Edomawa, wato zuriyar Isuwa, sun ce, “An rurrushe garuruwanmu, amma za su sāke gina su.” Sa'an nan Ubangiji zai amsa, ya ce, “To, su gina mana, ai, zan sāke rurrushe su. Mutane za su ce da ƙasarsu, ‘Ƙasar mugaye, da al'ummar da Ubangiji yake fushi da ita har abada.’ ”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan