Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 4:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Ki yi farin ciki, ki yi murna, ke Edom, Wadda kike zaune cikin ƙasar Uz. Amma fa za a ba ki ƙoƙo ki sha, Ki bugu har ki yi tsiraici.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Ku yi murna da farin ciki, ya Diyar Edom, ke mai zama a ƙasar Uz. Amma ke ma za a ba ki kwaf; za ki bugu ki zama tsirara.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 4:21
24 Iomraidhean Croise  

Waɗannan su ne 'ya'yan Dishan, maza, Uz da Aran.


Ubangiji kuwa ya ƙasƙantar da Yahuza, saboda Ahaz Sarkin Yahuza ya yi ganganci a Yahuza, ya zama marar aminci ga Ubangiji.


Akwai wani mutum a ƙasar Uz, mai suna Ayuba, amintacce ne, mai tsoron Allah. Shi mutumin kirki ne, natsattse, yana ƙin aikata kowace irin mugunta.


Ka tuna, ya Ubangiji, da abin da Edomawa suka yi, A ranar da aka ci Urushalima. Ka tuna da yadda suka ce, “A ragargaza ta har ƙasa!”


Ya saurayi! Ka yi murna a lokacin ƙuruciyarka, ka bar zuciyarka ta yi farin ciki a kwanakin samartakarka. Ka bi nufin zuciyarka da sha'awar idanunka. Amma ka sani fa, a cikin al'amuran nan duka Allah zai shara'anta ka.


Ubangiji ya ce, “Ga shi, waɗanda ba a shara'anta su ga shan ƙoƙon hukunci ba, za su sha shi, to, kai za ka kuɓuta? Ba za ka kuɓuta ba, amma lalle za ka sha shi!


Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya faɗa a kan Edom, “Ba hikima kuma a cikin Teman? Shawara ta lalace a wurin masu basira? Hikima ta lalace ne?


Gama Ubangiji Allah ya ce, “Da yake kun tafa hannuwanku, kun buga ƙafafunku, kuka yi murna don nuna dukan ƙiyayyarku da ƙasar Isra'ila,


Ubangiji Allah ya ce, “Da yake Mowab da Seyir sun ce mutanen Yahuza sun zama kamar al'ummai,


“Ɗan mutum, da yake Taya ta yi magana a kan Urushalima ta ce, ‘Madalla, Urushalima ta rushe, ƙofa ta buɗu, yanzu zan wadata da yake ta zama kufai,’


Ubangiji ya ce, “Mutanen Edom sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun farauci 'yan'uwansu, Isra'ilawa, Suka ƙi su nuna musu jinƙai. Ba su yarda su huce daga fushinsu ba.


Annabcin Obadiya ke nan. Wannan shi ne abin da Ubangiji Allah ya ce a kan al'ummar Edom. Ubangiji ya aiki manzonsa wurin sauran al'umma, Mun kuwa ji saƙonsa cewa, “Ku zo! Mu tafi mu yi yaƙi da Edom!”


Ku mazaunan Shafir, ku wuce abinku da tsiraici da kunya. Mazaunan Za'anan ba su tsira ba. Bet-ezel ta yi kururuwa, “Zai tumɓuke harasashin gininki.”


A maimakon daraja, za ka sha ƙasƙanci. Ka sha kai da kanka, ka yi tangaɗi. Ƙoƙon da yake a hannun Ubangiji zai faɗo a kanka, Kunya za ta rufe darajarka.


(“Ga ni nan a tafe kamar ɓarawo! Albarka tā tabbata ga wanda yake a zaune a faɗake, yana saye da tufafinsa, don kada ya tafi tsirara, a ga tsiraicinsa.”)


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan