Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 4:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Shi wanda muke dogara gare shi, Wato zaɓaɓɓe na Ubangiji, ya auka cikin raminsu, Shi wanda muka ce, “A ƙarƙashin inuwarsa ne za mu zauna a cikin sauran al'umma.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Shafaffe na Ubangiji, numfashin ranmu, ya fāɗi cikin tarkonsu. Muna tunani cewa za mu iya rayuwa cikin sauran mutane a ƙarƙashin inuwarsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 4:20
27 Iomraidhean Croise  

Sa'an nan Ubangiji Allah ya siffata mutum daga turɓayar ƙasa, a cikin kafafen hancinsa kuwa ya hura numfashin rai, mutum kuma ya zama rayayyen taliki.


“Domin haka kuwa, yanzu, idan na koma wurin baranka, mahaifina, ba tare da saurayin ba, in har bai ga yaron tare da ni ba, zai mutu, gama ransa ya shaƙu da saurayin, barorinka kuwa za su sa baranka, mahaifinmu, ya mutu cikin baƙin ciki, da tsufansa.


Dawuda ya ce, “Me ya sa ba ka ji tsoro ka miƙa hannunka, ka hallaka wanda Ubangiji ya keɓe ba?”


“Kada ruwan sama ko raɓa su zubo kan tuddan Gilbowa. Da ma gonakinta su zama marasa ba da amfani. Gama a can ne aka zube garkuwoyin jarumawa a wulakance, Tsatsa ta rufe garkuwar Saul.


Amma sojojin suka ce, “Ba za ka tafi tare da mu ba, gama idan muka gudu, ba za su kula da mu ba. Ko rabinmu sun mutu, ba za su kula ba, gama kai kana bakin mutum dubu goma (10,000) na mutanenmu. Zai fi kyau kuma ka zauna cikin gari ka riƙa aika mana da taimako.”


Abishai ɗan Zeruya kuwa ya ce, “Ya kamata a kashe Shimai gama ya zagi wanda Ubangiji ya zaɓa ya zama sarki.”


Irmiya kuma ya hurta makoki domin Yosiya. Haka nan kuma dukan mawaƙa mata da maza, suka ambaci Yosiya cikin makokinsu har yau. Suka sa waɗannan su zama farali a Isra'ila, ga shi kuma, an rubuta su a Littafin Makoki.


Ko wannensu zai zama kamar wurin fakewa daga iska da kuma wurin ɓuya saboda hadiri, za su zama kamar rafuffukan da suke gudu cikin hamada, kamar inuwar babban dutse a ƙeƙasasshiyar ƙasa.


Amma sojojin Kaldiyawa suka bi su, suka ci wa Zadakiya a filayen Yariko. Suka kama shi, suka kawo shi gaban Sarkin Babila a Ribla a ƙasar Hamat, a can Nebukadnezzar ya yanka masa hukunci.


Amma sojojin Kaldiyawa suka runtumi sarki Zadakiya, suka ci masa a filayen Yariko. Dukan sojoji suka yashe shi.


Da aka kama Zadakiya, sai aka kai shi wurin Sarkin Babila a Ribla a ƙasar Hamat, a nan ne Sarkin Babila ya yanke masa shari'a.


Ƙofofinta sun nutse ƙasa, Ya lalatar, ya kakkarya ƙyamarenta, An kai sarkinta da mahukuntanta cikin al'ummai, Inda ba a bin dokokin annabawanta, Ba su kuma samun wahayi daga wurin Ubangiji.


Zan yarɓa masa ragata in kama shi. Zan kai shi Babila, wato ƙasar Kaldiyawa, duk da haka ba zai gan ta ba, ko da yake zai rasu a can.


Bai kuwa cika rantsuwarsa da alkawarinsa ba. Ya ƙulla alkawari, amma ga shi, ya aikata dukan waɗannan abubuwa, ba zai kuɓuta ba.


Su kuma suka gangara tare da shi zuwa lahira, suka tarar da waɗanda aka kashe da takobi, wato waɗanda daga cikin al'ummai suka yi zama a inuwarsa.


Yana da ganyaye masu kyau Da 'ya'ya jingim don kowa da kowa ya ci. Namomin jeji suka sami inuwa a ƙarƙashinsa, Tsuntsayen sama kuma suka zauna a rassansa. Dukan masu rai a gare shi suka sami abinci.


Yanzu ina sarkinku da zai cece ku? Ina kuma dukan shugabanninku da za su kāre ku? Su waɗanda kuka roƙa, kun ce, ‘Ku naɗa mana sarki da shugabanni.’


Itacen ƙaya kuwa ya ce wa itatuwan, ‘In da gaske kuke, kuna so ku naɗa ni sarkinku, to, sai ku zo, ku fake a inuwata, in ba haka ba kuwa, bari wuta ta fito daga itacen ƙaya ta cinye itacen al'ul na Lebanon.’ ”


To, ga ni nan, ku shaida a kaina a gaban Ubangiji da gaban wanda Ubangiji ya naɗa sarki. Takarkari ko jakin wa na ƙwace? Wa kuma na zalunta, ko na wulakanta? A wurin wa na karɓi hanci don in danne gaskiya? Sai ku shaida, ni kuwa zan mayar masa.”


Sa'an nan ya ce musu, “Ubangiji shi ne shaida, wanda kuma ya naɗa, shi ma shaida ne a yau, cewa ba ku iske ni da laifin kome ba.” Jama'ar suka ce, “Ubangiji ne shaida.”


Da suka isa wurin hadayar, Sama'ila ya ga Eliyab, ɗan Yesse, sai ya zaci shi ne wanda Ubangiji ya zaɓa.


To, yau da idanunka ka ga yadda Ubangiji ya bashe ka a hannuna a kogon, har waɗansu suka ce mini in kashe ka, amma na ji tausayinka. Na ce, ‘Ba zan miƙa hannuna in kashe ubangijina ba, gama shi keɓaɓɓe na Ubangiji ne.’


Ya ce wa mutanensa, “Ubangiji ya sawwaƙa in yi wa ubangijina irin abu haka, har in miƙa hannuna in kashe keɓaɓɓe na Ubangiji.”


Abin da ka yi ba shi da kyau. Ka isa a kashe ka, da yake ba ka lura da mai girma ba, wanda Ubangiji ya keɓe. Ka duba, ina mashin sarki da butar ruwan da yake wajen kansa suke?”


Amma Dawuda ya ce wa Abishai, “Kada ka hallaka shi, gama wa zai taɓa wanda Ubangiji ya keɓe, ya rasa yin laifi?


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan