Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 4:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Masu runtumarmu sun fi gaggafar da take tashi sama sauri. Sun fafare mu a kan duwatsu, Suna fakonmu a cikin jeji.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Masu fafarar mu sun fi gaggafa mai firiya a sararin sama sauri; sun fafare mu a kan duwatsu suna fakon mu a jeji.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 4:19
13 Iomraidhean Croise  

“Ga shi, ina aiko da masunta da yawa,” in ji Ubangiji, “za su kuwa kama su, daga baya kuma zan aika da mafarauta da yawa, za su farauce su daga kowane tsauni, da tudu, da kogwannin duwatsu.


Duba, ga abokin gāba yana zuwa kamar gizagizai, Karusan yaƙinsa suna kama da guguwa, Dawakansa sun fi gaggafa sauri. Kaitonmu, mun shiga uku!


“Daga sama ya aukar da wuta a cikin ƙasusuwana. Ya kuma kafa wa ƙafafuna ashibta, Ya komar da ni baya, Ya bar ni a yashe, sumamme dukan yini.


Ubangiji ya ce, “Ki sa ƙaho a bakinki, Kamar gaggafa, haka maƙiyi ya kawo sura a kan ƙasar Ubangiji, Domin mutanena sun ta da alkawarina, Sun kuma keta dokokina.


Isra'ila ta ƙi abin da yake mai kyau, Don haka abokan gāba sun fafare ta.


“Amma ga waɗanda suka ragu, zan sa fargaba a zuciyarsu sa'ad da suke a ƙasar maƙiyansu. Ko motsin ganye kawai ma zai razanar da su su sheƙa a guje kamar waɗanda ake fafara da takobi, ga shi kuwa, ba mai korarsu, za su kuwa fāɗi.


Ko masu saurin gudu ma ba za su tsere ba, Ƙarfafa za su zama kumamai, Sojoji kuma ba za su iya ceton kansu ba.


“Dawakansu sun fi damisa sauri, Sun fi kyarketan maraice zafin hali, Sojojin dawakansu suna zuwa a guje. Sojojin dawakansu suna zuwa daga nesa, Sukan tashi kamar gaggafa da sauri don su cinye.


Ubangiji zai kawo wata al'umma daga nesa, wato daga bangon duniya, mai kai sura kamar gaggafa, wadda za ta yi gāba da ku. Al'ummar da ba ku san harshenta ba,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan