Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 4:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Ana bin sawayenmu, Don haka ba mu iya tafiya a titunanmu ba. Ƙarshenmu ya yi kusa, Kwanakinmu sun ƙare, Gama ƙarshenmu ya zo.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Ana bin sawunmu, ba za mu iya tafiya kan tituna ba. Ƙarshenmu ya kusa, kwanakinmu sun ƙare, gama ƙarshenmu ya zo.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 4:18
16 Iomraidhean Croise  

Da zan ci nasara a kan kowane abu, Da sai ka yi ta farautata kamar zaki, Kana aikata al'ajabai don ka cuce ni.


Ka sa waɗanda suke saran waɗansu a ƙaryace, Kada su yi nasara. Ka sa mugunta ta hallaka mutumin da yake ta da zaune tsaye.”


Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ka gani sosai, gama zan lura da maganata don in cika ta.”


“Ga shi, ina aiko da masunta da yawa,” in ji Ubangiji, “za su kuwa kama su, daga baya kuma zan aika da mafarauta da yawa, za su farauce su daga kowane tsauni, da tudu, da kogwannin duwatsu.


A sa'ad da ya isa Ƙofar Biliyaminu, shugaban matsara, Irija ɗan Shelemiya, ɗan Hananiya, ya kama annabi Irmiya ya ce, “Kai kana gudu zuwa wurin Kaldiyawa ne.”


Annabawa sun yi annabcin ƙarya, Firistoci kuma sun yi mulki da ikon kansu, Mutanena kuwa suna so haka! Amma sa'ad da ƙarshe ya zo, me za ku yi?”


Ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila na ce, “Mutanen Babila sun zama kamar daɓen masussuka A lokacin da ake sussuka, Ba kuwa da daɗewa ba lokacin girbe ta zai zo.”


“Waɗanda suke maƙiyana ba dalili Sun farauce ni kamar tsuntsu.


“Ɗan mutum, ga shi, mutanen Isra'ila suna cewa, ‘Wahayin da ya gani na wani lokaci ne can gaba, yana annabci a kan wani zamani ne na can.’


Sai Ubangiji ya ce, “Amos, me ka gani?” Na ce, “Kwandon ɓaure na ci.” Ubangiji kuma ya ce mini, “Ƙarshen jama'ata Isra'ila ya zo. Ba zan sāke nufina a kan yi musu hukunci ba.


Shin, sawun wa Sarkin Isra'ila yake bi? Wane ne kuma kake runtuma? Kana bin sawun mataccen kare, da sawun tunkuyau?


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan