Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 4:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Idanunmu sun gaji Da zuba ido a banza don samun taimako, Mun zuba ido Ga al'ummar da ba za ta iya cetonmu ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Idanunmu sun gaji, suna ta dubawa ko taimako zai zo; mu sa ido ko za mu ga ƙasar da za tă iya taimakon mu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 4:17
15 Iomraidhean Croise  

Sarkin Masar kuma bai sāke fitowa daga Masar ba, gama Sarkin Babila ya ƙwace dukan ƙasar da take ta Sarkin Masar, tun daga rafin Masar har zuwa Kogin Yufiretis.


Waɗanda suke dogara ga Habasha, suna kuwa fāriya da Masar, za su ruɗe, sa zuciyarsu zai wargaje.


Alkawarin da kuka ƙulla da mutuwa ya tashi, yarjejeniyar da kuka yi da lahira, an soke ta. Sa'ad da masifa ta auko za a hallaka ku.


Wace riba ka samu, har da ka tafi Masar, Don ka sha ruwan Kogin Nilu? Wace riba ka samu, har da ka tafi Assuriya, Don ka sha ruwan Kogin Yufiretis?


Me ya sa ba ku da tsayayyiyar zuciya, Sai ku yi nan ku yi can? Masar za ta kunyata ku kamar yadda Assuriya ta yi.


Da hannuwanku a kā za ku komo daga Masar don kunya. Gama waɗanda kuke dogara gare su, ni Ubangiji, na ƙi su, Ba za ku yi arziki tare da su ba.”


Mutane suna ta cewa, “Damuna ta ƙare, kaka kuma ta wuce, Amma ba a cece mu ba.”


“Na kira masoyana, amma suka yaudare ni, Firistocina da dattawana a cikin birni sun hallaka Saboda neman abincin da za su ci su rayu.


A kwanakin wahalarta na rashin wurin zama, Urushalima ta tuna da dukan abubuwanta masu daraja a dā. A lokacin da mutanenta suka fāɗa a hannun maƙiyi, Ba wanda ya taimake ta, Maƙiyanta sun gan ta, Sun yi mata ba'a saboda fāɗuwarta.


Mun miƙa hannu ga Masar da Assuriya Don mu sami abinci.


Ba za su ƙara zama abin dogara ga mutanen Isra'ila ba, gama Isra'ilawa za su tuna da laifin suka yi, suka nemi taimakon Masarawa. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji Allah.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan