Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 4:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Ubangiji kansa ya watsar da su, Ba zai ƙara kulawa da su ba. Ba su darajanta firistoci ba, Ba su kuma kula da dattawa ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Ubangiji kansa ya warwatsa su; ya daina duban su. Ba a ba firistoci girma, ba su ba dattawa gata.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 4:16
20 Iomraidhean Croise  

La'ananne ne fushinsu domin mai tsanani ne, Da hasalarsu kuma, gama bala'i ce. Zan warwatsa su cikin dukan ƙasar Yakubu, In ɗaiɗaitar su su cikin Isra'ilawa.


Don haka Ubangiji ya bashe su ga Sarkin Kaldiyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a Haikali, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka a hannunsa.


Zai warwatsa zuriyarsu a cikin arna, Ya bar su su mutu a baƙuwar ƙasa.


Duk da haka Ubangiji ya ji su sa'ad da suka yi kira gare shi, Ya kula da wahalarsu.


Bala'i ɗaya ne zai sami kowa da kowa, firistoci da sauran jama'a, bayi da iyayengijinsu, masu saye da masu sayarwa, masu ba da rance da masu karɓa, attajirai da matalauta.


Na yi fushi da mutanena, Na maishe su kamar su ba nawa ba ne. Na sa su a ƙarƙashin ikonki, Ba ki kuwa yi musu jinƙai ba, Har da tsofaffi ma kin ba su wuya.


Zan kuma sa su zama abin banƙyama ga dukan mulkokin duniya saboda abin da Manassa ɗan Hezekiya, Sarkin Yahuza ya aikata a Urushalima.


Zan maishe su abin ƙyama da masifa ga mulkokin duniya duka. Za su zama abin zargi, da karin magana, da ba'a, da la'ana a dukan wuraren da zan warwatsa su.


Shugaban matsara kuma ya ɗauki Seraiya babban firist, da Zafaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofar Haikali, ya tafi da su.


Ya Ubangiji, ka duba, ka gani! Wane ne ka yi wa haka? Mata za su cinye 'ya'yansu da suke reno? Ko kuwa za a kashe firist da annabi A cikin Haikalin Ubangiji?


Ya rushe Haikalinsa kamar bukka cikin gona, Ya mai da wurin yin ƙayyadaddun idodinsa kufai. Ubangiji ya sa ƙayyadadden idi da kiyaye Asabar Su ƙare a Sihiyona, Da zafin fushinsa kuma ya wofinta sarki da firist.


An rataye shugabanni da hannuwansu, Ba a kuma girmama dattawa ba.


Ubanni za su cinye 'ya'yansu, 'ya'ya kuma za su cinye ubanninsu. Zan hukunta ki, waɗanda kuma suka tsira zan watsar da su ko'ina.


“Ubangiji zai sa abokan gabanku su rinjaye ku cikin yaƙi. Ta hanya guda za ku auka musu, amma ta hanyoyi bakwai za ku gudu daga gabansu. Za ku zama abin ƙi ga dukan mulkokin duniya.


Na ce, zan watsar da su, in sa a manta da su cikin mutane.


Ba irin alkawarin da na yi da kakanninsu ba, A ranar da na kama hannunsu Domin in fito da su daga ƙasar Masar. Saboda ba su tsaya ga alkawarina ba, Shi ya sa na ƙyale su, in ji Ubangiji.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan