Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 4:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Sun yi ta kai da kawowa a titi kamar makafi, Sun ƙazantu da jini Har ba wanda zai taɓa rigunansu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Yanzu suna yawo barkatai a tituna kamar makafi. Sun ƙazantu da jini yadda ba wanda zai kuskura ya taɓa rigunansu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 4:14
15 Iomraidhean Croise  

“Sa'ad da kuke ɗaga hannuwanku wajen yin addu'a, ba zan dube ku ba. Kome yawan addu'ar da kuka yi, ba zan kasa kunne ba domin zunubi ya ɓata hannuwanku.


Matsaransa makafi ne, dukansu marasa ilimi ne. Dukansu kamar karnuka ne bebaye, ba su iya haushi ba, suna kwance suna ta mafarki, suna jin daɗin rurumi!


Tufafinku sun ƙasantu da jinin marasa laifi, Waɗanda ba ku same su suna fasa gidajenku ba. Amma duk da haka kuna cewa,


Sa'ad da Irmiya ya gama faɗar dukan abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa wa dukan jama'a, sai firistoci, da annabawa, da dukan jama'a suka kama shi, suna cewa, “Mutuwa za ka yi!


Amma adalai za su yanka musu hukunci irin wanda akan yi wa mata mazinata, da mata masu kisankai, gama su mazinata ne masu kisankai.


Akwai rantsuwa, da ƙarya, da kisankai, da sata, da zina, Da kama-karya, da zub da jini a kai a kai.


“Zan aukar wa mutane da wahala, Za su kuwa yi tafiya kamar makafi, Domin sun yi wa Ubangiji zunubi. Za a zubar da jininsu kamar ƙura, Namansu kuwa kamar taroso.”


Wanda duk yake cikin saura ya taɓa wanda aka kashe da tokobi, ko gawa, ko ƙashin mutum, ko kabari zai ƙazantu har kwana bakwai.


Saboda haka kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zaune a ciki, gama jini yakan ƙazantar da ƙasa. Ba wata kafara da za a yi don ƙasar da aka zubar da jini a cikinta, sai dai da jinin wanda ya zubar da jinin.


Ƙyale su kawai, makafin jagora ne. In kuwa makaho ya yi wa makaho jagora, ai, duk biyu sai su faɗa a rami.”


Duhun zuciya yake a gare su, bare suke ga rai wanda Allah yake bayarwa, sabili da jahilcin da yake a gare su, saboda taurin kansu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan