Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 4:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Dalili kuwa saboda zunuban annabawa ne, Da muguntar firistoci, Waɗanda suka kashe adalai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Amma ya faru domin zunuban annabawanta da muguntar firistocinta, waɗanda suka zub da jinin masu adalci a cikinsu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 4:13
18 Iomraidhean Croise  

Ubangiji kuwa ya ce mini, “Annabawa, annabcin ƙarya suka yi da sunana. Ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba, ban kuma yi magana da su ba. Annabcin da suke yi muku na wahayin ƙarya ne, dubar da suke yi marar amfani ce, tunaninsu ne kawai.


“Ya Isra'ila, tun da daɗewa, ka ƙi yarda Ubangiji ya mallake ka, Ka ƙi yin biyayya da ni, Ka kuwa ce, ‘Ba zan yi bauta ba.’ Amma ka yi karuwanci a kan kowane tudu, Da kowane ɗanyen itace.


Na hori 'ya'yanku, amma a banza, ba su horu ba, Kun kashe annabawanku da takobi kamar mayunwacin zaki.


Annabawa sun yi annabcin ƙarya, Firistoci kuma sun yi mulki da ikon kansu, Mutanena kuwa suna so haka! Amma sa'ad da ƙarshe ya zo, me za ku yi?”


Gama daga ƙaraminsu zuwa babba, Kowannensu yana haɗama ya ci ƙazamar riba, Har annabawa da firistoci, Kowannensu ya shiga aikata rashin gaskiya.


Annabawanki sun gano miki wahayan ƙarya, Ba su tone asirin muguntarki, Har da za a komo da ke daga bauta ba. Amma suka yi miki annabcin ƙarya na banza.


Kun kashe mutane da yawa a wannan birni, har kun cika titunansa da gawawwaki.’


Annabawanta suna kama da zakoki masu ruri waɗanda suke yayyage ganimar da suka samu. Sun kashe mutane, sun ƙwace dukiya da abubuwa masu daraja. Sun sa mata da yawa sun rasa mazansu.


Ta haka kuka shaidi kanku ku ne 'ya'yan masu kisan annabawa.


A cikin annabawa wane ne kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun kuma kashe waɗanda suka yi faɗi a kan zuwan Mai Adalcin nan, wanda a yanzu kuka zama maciya amanarsa, da kuma makasansa,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan