Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 4:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Ubangiji ya saki fushinsa, Ya zuba fushinsa mai zafi. Ya kunna wa Sihiyona wuta Wadda ta cinye harsashin gininta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Ubangiji ya saki fushinsa; ya zuba zafin fushinsa. Ya hura wuta a Sihiyona ta kuma cinye harsashin gininta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 4:11
29 Iomraidhean Croise  

A kan kusurwar kowane titi Mutanenki sun rafke saboda rashin ƙarfi, Sun zama kamar barewa da tarkon maharbi ya kama. Suka ji ƙarfin fushin Allah.


Zan sa su kara da junansu, iyaye maza da 'ya'yansu maza, in ji Ubangiji. Tausayi, ko juyayi, ko jinƙai ba za su sa in fasa hallaka su duka ba.’ ”


Amma idan ba ku kasa kunne gare ni ba, ba ku kuwa kiyaye ranar Asabar da tsarki ba, kun kuma ɗauki kaya kun shiga ta ƙofofin Urushalima a ranar Asabar, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wuta. Za ta kuwa cinye fādodin Urushalima, ba kuwa za ta kasu ba.’ ”


Zan hukunta ku bisa ga ayyukanku,’ in ji Ubangiji, ‘Zan sa wa jejin ƙasar wuta. Za ta cinye duk abin da yake kewaye da ita.’ ”


Mai yiwuwa ne za su roƙi Ubangiji, su tuba, su bar mugayen ayyukansu, gama Ubangiji yana fushi ƙwarai, Ubangiji ya hurta hasala a kan wannan jama'a.”


Saboda haka ga abin da Ubangiji Allah ya ce, “Duba, zan kwarara fushina da hasalata a kan wannan wuri, a kan mutum duk da dabba, da akan itatuwan saura da amfanin gona. Zai yi ta cin wuta, ba kuwa za a kashe ba.”


Ubangiji ya duhunta Sihiyona saboda fushinsa! Daga Sama kuma ya jefar da darajar Isra'ila a ƙasa. Bai kuma tuna da matashin sawayensa ba A ranar fushinsa.


Ubangiji ya aikata abin da ya yi niyya, Ya cika maganarsa wadda ya faɗa tun dā, Ya hallakar, ba tausayi, Ya sa maƙiyi ya yi murna a kanki, Ya ƙarfafa ƙarfin maƙiyanki.


Da zafin fushinsa, ya karya ƙarfin Isra'ila, Ya kuma bar yi musu taimako A lokacin da abokan gāba suka zo. Kamar harshen wuta, ya ƙone dukan abin da yake na Yakubu.


Ya ja bakansa kamar abokan gāba, Ya kuma nuna ikonsa kamar maƙiyi. Ya hallaka dukan abin da yake da bansha'awa. A alfarwar Sihiyona, ya zubo da hasalarsa kamar wuta.


Ubangiji ya yi niyya Ya mai da garun Sihiyona kufai, Ya auna ta da igiyar awo, Bai janye dantsensa daga hallaka ta ba. Ya sa kagara da garu su zozaye, su lalace tare.


Ya Sihiyona, hukunci a kan muguntarki ya ƙare, Ba zai ƙara barinki a ƙasar bauta ba. Amma zai hukunta ki saboda muguntarki, ya Edom, Zai tone zunubanki.


Saboda haka na kwarara musu fushina, na ƙone su da wutar hasalata, na ɗora alhakin ayyukansu a bisa kawunansu, ni Ubangiji Allah na faɗa.”


Sai na husata da su saboda jinin da suka zuba a cikin ƙasar, da kuma yadda suka ƙazantar da ƙasar da gumakansu.


Annoba za ta kashe wanda yake nesa, wanda yake kusa kuwa takobi zai kashe shi. Yunwa kuma za ta kashe wanda yaƙi ya kewaye shi. Ta haka zan aukar da fushina a kansu.


Ya tabbatar da maganarsa wadda ya yi a kanmu da shugabanninmu waɗanda suka yi mulkinmu. Ya aukar mana da babban bala'i, gama a duniya duka ba a taɓa yin irin abin da aka yi wa Urushalima ba.


sai ni ma in tayar muku da fushi, in hukunta ku har riɓi bakwai, saboda zunubanku.


Kafin a zartar da umarni, Kafin a kore ku kamar ƙaiƙayi, Kafin kuma zafin fushin Ubangiji ya auko muku, Kafin ranar hasalar Ubangiji ta auko muku.


Amma maganata da dokokina waɗanda na umarta wa bayina annabawa, sun tabbata a kan kakanninku, sai suka tuba, suka ce, ‘Kamar yadda Ubangiji Mai Runduna ya yi niyya ya yi da mu saboda hanyoyinmu da ayyukanmu, haka kuwa ya yi da mu.’ ”


Saboda lokacin sakamako ne, don a cika duk abin da yake rubuce.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan