Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 4:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Ƙaƙa zinariya ta zama duhu! Ƙaƙa zinariya tsantsa ta sāke! Tsarkakakkun duwatsu kuma suna zube A kowane magamin titi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Zinariya ta rasa kyanta, hasken zinariya ya dushe! An warwatsar da tsarkakakkun duwatsu masu daraja a kan tituna.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 4:1
11 Iomraidhean Croise  

Birnin da yake dā mai aminci ne, yanzu ya zama kamar karuwa! Dā adalai a can suke zaune, amma yanzu sai masu kisankai kaɗai.


Ya Sarkin Babila, kai da kake tauraron asubahi mai haske, ka fāɗo daga sama. A dā ka ci al'ummai da yaƙi amma yanzu an fyaɗa ka ƙasa.


Sai ya ƙone Haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan manyan gidajen da suke Urushalima.


Ki tashi, ki ya ta kuka dukan dare, Ki bulbule abin da yake cikin zuciyarki Kamar ruwa gaban Ubangiji. Ki miƙa hannuwanki zuwa gare shi, Saboda rayukan 'ya'yanki, Waɗanda suke suma da yunwa A magamin kowane titi!


“Ɗan mutum, mutanen Isra'ila sun zama kamar ƙwan maƙera a gare ni. Dukansu sun zama kamar tagulla, da kuza, da baƙin ƙarfe, da darma, a tanderu, sun zama ƙwan maƙera na azurfa.


“Domin haka zan mai da Samariya jujin kufai a karkara, Wurin dasa kurangar inabi. Zan zubar da duwatsunta a cikin kwari, In tone harsashin gininta.


Amma ya amsa musu ya ce, “Kun ga duk waɗannan ko? Hakika, ina gaya muku, ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan'uwansa ba a baje shi ba.”


Sai Yesu ya ce masa, “Ka ga manyan gine-ginen nan? Ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan'uwansa, da ba za a baje shi ba.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan