Ya aika da iska a gabansa kamar rigyawa wadda take kwashe kome, ta tafi da shi. Yakan gwada al'ummai ya kai su hallaka, yakan sa dukan shirye-shiryensu na mugunta su ƙare.
Don me ka bari muka ɓata daga al'amuranka? Don me ka bari muka taurare, har muka bar binka? Ka komo, domin darajar waɗanda suke bauta maka, domin kuma mutanen da suke naka ne a koyaushe.