Sai suka ɗauki Irmiya suka saka shi a rijiyar Malkiya ɗan sarki, wadda take gidan waƙafi. Suka zurara Irmiya a ciki da igiya. Ba ruwa a rijiyar, sai dai lāka, Irmiya ya nutse cikin lākar.
Yau na kwance ƙuƙumin da yake a wuyanka, idan ka ga ya fi maka kyau, ka zo mu tafi tare zuwa Babila, to, sai ka zo, zan lura da kai da kyau, amma idan ba ka ga haka ya yi maka daidai ba, to, kada ka bi ni. Ga dukan ƙasa shimfiɗe a gabanka, ka tafi duk inda ka ga ya fi maka kyau.”
“Ubangiji ya tattara laifofina Ya yi karkiya da su, Ya ɗaura su a wuyana, Ya sa ƙarfina ya kāsa. Ya kuma bashe ni a hannun Waɗanda ban iya kome da su ba.
Ya tabbatar da maganarsa wadda ya yi a kanmu da shugabanninmu waɗanda suka yi mulkinmu. Ya aukar mana da babban bala'i, gama a duniya duka ba a taɓa yin irin abin da aka yi wa Urushalima ba.