61 “Ya Ubangiji, ka ji zargi Da dukan dabarun da suke yi mini.
61 Ya Ubangiji, ka ji zaginsu, da duka mugun shirin da suke yi mini
Amma ka tuna fa, ya Ubangiji, abokan gābanka suna yi maka ba'a, Su wawaye ne waɗanda suke raina ka.
Kada ka manta da yadda aka ci mutuncina, ni da nake bawanka, Da yadda na daure da dukan cin mutuncin da arna suka yi mini.
Amma ya Ubangiji, Ka san dukan maƙarƙashiyarsu, su kashe ni, Kada ka gafarta musu muguntarsu, kada kuma ka shafe zunubinsu daga gabanka. Ka sa a jefar da su daga gabanka, Ka yi da su sa'ad da kake fushi!”
Bari ya yarda a mari kumatunsa, Ya haƙura da cin mutunci.
Ya Ubangiji, ka tuna da abin da ya same mu. Ka duba, ka ga yadda muka zama abin kunya!
“Na ji ba'ar da Mowab ta yi, da zagin Ammonawa, Yadda suka yi wa mutanena ba'a, Sun yi alwashi, cewa za su cinye ƙasarsu.