Amma kana gani, kana kuma lura da masu shan wuya, da masu ɓacin rai, Koyaushe kuma a shirye kake ka yi taimako. Mutum wanda ba shi da mai taimako yakan danka kansa gare ka, Gama kullum kakan taimaki masu bukata.
Amma ya Ubangiji, Ka san dukan maƙarƙashiyarsu, su kashe ni, Kada ka gafarta musu muguntarsu, kada kuma ka shafe zunubinsu daga gabanka. Ka sa a jefar da su daga gabanka, Ka yi da su sa'ad da kake fushi!”