6 Ya zaunar da ni cikin duhu, Kamar waɗanda suka daɗe da mutuwa.
6 Ya sa na zauna a cikin duhu kamar waɗanda suka mutu da jimawa.
Maƙiyina ya tsananta mini, Ya kore ni fata-fata. Ya sa ni a kurkuku mai duhu, Ina kama da waɗanda suka daɗe da mutuwa,
Yanzu ka amsa mini, ya Ubangiji! Na fid da zuciya duka! Kada ka ɓuya mini, Don kada in zama cikin waɗanda suke gangarawa zuwa lahira.
Muna ta lalubar bango kamar makafi, muna ta lalubawa kamar marasa idanu. Da tsakar rana muke ta tuntuɓe, sai ka ce da almuru. A tsakanin waɗanda suke da cikakken ƙarfi, kamar matattu muke.