Da daren nan Ubangiji ya bayyana gare shi ya ce, “Ni ne Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai, zan sa maka albarka in riɓaɓɓanya zuriyarka saboda bawana Ibrahim.”
sai ya aike da amsa, ya ce musu, “Ku faɗa wa ubangidanku, Ubangiji ya ce, ‘Kada ka ji tsoron maganganun da ka ji daga bakin barorin Sarkin Assuriya, waɗanda suka saɓe ni.
Sa'an nan za ku yi kira, ni kuwa zan amsa, za ku yi kuka, ni kuwa zan ce muku, ‘Ga ni.’ “Idan kuka kawar da karkiya daga cikinku, kuka daina nuna wa juna yatsa, da faɗar mugayen maganganu,
Kada ka ji tsoron wuyar da za ka sha. Ga shi, Iblis yana shiri ya jefa waɗansunku a kurkuku don a gwada ku, za ku kuwa sha tsanani har kwana goma. Ka riƙi amana ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka kambin rai.