54 Ruwa ya sha kaina, Sai na ce, ‘Na halaka.’
54 ruwaye suka rufe kaina, sai na yi tunani cewa na kusa mutuwa.
An yi duhu ƙwarai, har ba ka iya gani, Rigyawa ta sha kanka.
Mutuwa ta ɗaure ni kam da igiyoyinta, Halaka ta auko mini a kai a kai.
Na ji tsoro, na zaci ka jefar da ni ne daga gabanka. Amma ka ji kukana sa'ad da na yi kira gare ka neman taimako.
Kada ka bar ambaliyar ruwa ta rufe ni. Kada ka bar ni in mutu cikin zurfafa, Ko in nutse a cikin kabari.
Hasalarka ta bi ta kaina, Tasar mini da kake ta yi, ta hallaka ni.
Aka kama shi, aka yanke masa shari'a, Aka tafi da shi domin a kashe shi, Ba wanda ya kula da ƙaddararsa. Aka kashe shi saboda zunubin mutanenmu.
Sai na ce, “Darajata ta ƙare, Ba ni kuma da sa zuciya wurin Ubangiji.”
Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum waɗannan ƙasusuwa su ne mutanen Isra'ila duka. Ga shi, suna cewa, ‘Ƙasusuwa sun bushe, zuciyarmu kuwa ta karai, an share mu ƙaƙaf.’
Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.