Domin haka ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Ga shi kuwa, zan hukunta su, za a kashe samarinsu da takobi, 'ya'yansu mata da maza, yunwa za ta kashe su.
Mutanen da suka yi wa annabci, za a jefar da su waje a kan titunan Urushalima, a karkashe su da yunwa da takobi, ba wanda zai binne su, da su, da matansu, da 'ya'yansu mata da maza. Zan sa muguntarsu ta koma kansu.
Idan na tafi cikin saura, Sai in ga waɗanda aka kashe da takobi! Idan kuma na shiga birni, Sai in ga waɗanda suke ta fama da yunwa! Gama annabi da firist, sai harkarsu suke ta yi a ƙasar, Amma ba su san abin da suke yi ba.’ ”
Zan sa su ci naman 'ya'yansu mata da maza. Kowa zai ci naman maƙwabcinsa cikin damuwa a lokacin da za a kewaye su da yaƙi, zai sha wahala daga wurin abokan gābansa da waɗanda suke neman ransa.’
Idanuna sun dushe saboda kuka, Raina yana cikin damuwa. Zuciyata ta karai saboda halakar mutanena, Gama 'yan yara da masu shan mama Sun suma a titunan birnin.