Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce a kan annabawa, “Ga shi, zan ciyar da su da abinci mai ɗaci, In shayar da su da ruwan dafi. Daga wurin annabawan Urushalima Rashin tsoron Allah ya fito ya mamaye dukan ƙasar.”
Mutanen Urushalima sun ce, “Don me muke zaune kawai? Bari mu tattaru, mu tafi cikin garuruwa masu garu, Mu mutu a can, Gama Ubangiji Allahnmu ya ƙaddara mana mutuwa, Ya ba mu ruwan dafi, Domin mun yi masa laifi.