Dukan masu wucewa suna yin miki tafin raini. Suna yi wa Urushalima tsāki, Suna kaɗa mata kai, suna cewa, “Ai, Urushalima ke nan, Birnin nan da ake cewa mai cikakken jamali, Wanda ya ƙayatar da dukan duniya?”
Ubangiji zai sa ku zama kai, ba wutsiya ba. Kullum ci gaba za ku yi, ba baya ba, idan kuka yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau, in kun lura, kun yi aiki da su,