Na ce, “Ya Allahna, kunya ta rufe fuskata, ban iya in ko ɗaga idanuna wajenka ba, gama muguntarmu ta sha kanmu, tsibin zunubanmu kuma ya kai har sammai.
“Amma suka yi maka rashin biyayya, suka tayar maka, Suka juya wa dokokinka baya, Suka karkashe anna bawan da suka faɗakar da su, Waɗanda suka faɗa musu su juyo gare ka. Suka yi ta saɓa maka lokaci lokaci.
Ke dai ki yarda da laifinki, Da kika yi wa Ubangiji Allahnki, Kin kuma watsar da mutuncinki a wurin baƙi A gindin kowane itace mai duhuwa. Kika ƙi yin biyayya da maganata, Ni, Ubangiji, na faɗa.
Ya Urushalima, tsatsarki ita ce ƙazantar lalatarki. Da yake na tsabtace ki, ba ki tsabtatu ba, To, ba za ki ƙara yin tsabta ba, Har lokacin da na fashe fushina a kanki.’
“Ya Ubangiji Allahnmu, kai ne ka fito da jama'arka daga ƙasar Masar da iko mai girma, da haka ka bayyana ikonka kamar yadda yake a yau, amma mun yi zunubi, mun aikata mugunta.
Amma maganata da dokokina waɗanda na umarta wa bayina annabawa, sun tabbata a kan kakanninku, sai suka tuba, suka ce, ‘Kamar yadda Ubangiji Mai Runduna ya yi niyya ya yi da mu saboda hanyoyinmu da ayyukanmu, haka kuwa ya yi da mu.’ ”