Gama haka wanda yake can Sama, Maɗaukaki, wanda ake kira Mai Tsarki ya ce, “Ina zaune a can Sama a tsattsarkan wuri, tare kuma da wanda yake da halin tuba mai tawali'u, don in farfaɗo da ruhun masu tawali'u, in kuma farfaɗo da zukatan masu tuba.
Saboda kuma muna Kaunarku ƙwarai da gaske ne shi ya sa muke jin daɗin ba da har rayukanmu ma saboda ku, ba yi muku bisharar Allah kaɗai ba, don kun shiga ranmu da gaske.