Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 3:40 - Littafi Mai Tsarki

40 Bari mu jarraba, mu bincika hanyoyinmu, Sa'an nan mu komo wurin Ubangiji.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

40 Bari mu auna tafiyarmu mu gwada ta, sai mu kuma koma ga Ubangiji.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 3:40
22 Iomraidhean Croise  

Sai mazanni suka tafi ko'ina da ina a dukan ƙasar Isra'ila da ta Yahuza da wasiƙu daga wurin sarki da sarakunansa, yadda sarki ya umarta. “Ya ku jama'ar Isra'ila, ku komo wurin Ubangiji Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Isra'ila domin ya sāke juyowa zuwa ga sauranku, waɗanda kuka kuɓuta daga hannun sarakunan Assuriya.


Gama idan kun juyo zuwa ga Ubangiji, 'yan'uwanku da 'ya'yanku za su sami rahamar waɗanda suka kama su, su komo wannan ƙasa. Gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne, mai jinƙai, ba zai kawar da fuskarsa daga gare ku ba, idan kun komo gare shi.”


Na yi tunani a kan ayyukana, Na yi alkawari in bi ka'idodinka.


Ku ji tsoro, ku daina aikata zunubinku, Ku yi tunani da gaske a kan wannan A kaɗaice, shiru, a ɗakunanku.


Bari mugaye su bar irin al'amuransu, Su sāke irin tunaninsu. Bari su juyo wurin Ubangiji, Allahnmu, Shi mai jinƙai ne, mai saurin gafartawa.


Domin ya yi tunani, ya bar laifofin da ya aikata, zai rayu, ba zai mutu ba.


Sai ku koma wurin Allahnku, Ku yi alheri, ku yi adalci, Ku saurari Allahnku kullayaumin.


“Zan koma wurin zamana Sai lokacin da suka yarda sun yi zunubi, su neme ni. A cikin ƙuncinsu za su neme ni.”


Mutane sun ce, “Zo, mu koma wurin Ubangiji, Gama shi ne ya yayyaga, Shi ne kuma zai warkar. Shi ne ya yi mana rauni, Shi ne kuma zai ɗaure raunin da maɗauri.


Da fari, na yi wa mutanen Dimashƙu wa'azi, sa'an nan na yi a Urushalima da dukan kewayen ƙasar Yahudiya, sa'an nan kuma na yi wa al'ummai, cewa su tuba su juyo ga Allah, su kuma yi aikin da zai nuna tubarsu.


Sai dai kowa ya auna kansa, sa'an nan ya ci gurasar, ya kuma sha a ƙoƙon.


Amma in da za mu auna kanmu sosai, da ba za a hukunta mu ba.


Ku jarraba kanku ku gani, ko har yanzu kuna a raye da bangaskiya. Ku riƙa auna kanku. Ashe, ba ku tabbata Almasihu yana a cikinku ba? Sai ko in kun kasa ga gwajin!


Sa'ad da wahala ta same ku, waɗannan abubuwa kuma suka auko muku nan gaba, za ku juyo wurin Ubangiji Allahnku, ku yi masa biyayya.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan