Da kwanakin makokin suka ƙare, sai Dawuda ya aika aka kawo ta gidansa, ta zama matarsa, ta haifa masa ɗa. Amma Ubangiji bai ji daɗin mugun abin nan da Dawuda ya yi ba.
Mai yiwuwa ne ka ce kai ba ruwanka, amma Allah ya sani, yana kuwa auna manufofinka. Yana lura da kai, ya kuwa sani. Yakan sāka wa mutane a kan abin da suke aikatawa.
Haka Ubangiji ya ce, ka yi gaskiya da adalci, ka ceci wanda ake masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka cuci baƙo, ko maraya, ko gwauruwa, wato matar da mijinta ya rasu, kada kuma ka zubar da jinin marasa laifi a wannan wuri.
Kai mai tsarki ne, Ka fi ƙarfin ka dubi mugunta. Kai da ba ka duban laifi. Me ya sa kake duban marasa imani? Kana iya shiru sa'ad da mugu yake haɗiye Mutumin da ya fi shi adalci?
“Idan wata gardama ta tashi tsakanin mutane, suka je gaban shari'a, alƙalai kuwa suka yanke musu maganar, suka kuɓutar da marar laifi, suka kā da mai laifin,