Zan ce wa 'yan kurkuku, ‘Ku tafi na sake ku!’ Waɗanda suke cikin duhu kuwa, in ce musu, ‘Ku fito zuwa wurin haske!’ Za su zama kamar tumakin da suke kiwo a tuddai,
“Isra'ilawa kamar tumaki ne waɗanda zakuna suka bi su suna kora. Da farko dai Sarkin Assuriya ne ya cinye su. Yanzu kuwa Sarkin Babila, wato Nebukadnezzar, shi ne yake gaigayi ƙasusuwansu.