Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 3:32 - Littafi Mai Tsarki

32 Ko da ya sa ɓacin rai, Zai ji tausayi kuma, Saboda tabbatacciyar ƙaunarsa mai yawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

32 Ko da ya kawo ɓacin rai, zai nuna tausayi sosai, ƙaunarsa tana da yawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 3:32
15 Iomraidhean Croise  

Amma Ubangiji ya nuna musu alheri, ya ji tausayinsu, bai ba su baya ba saboda alkawarinsa da Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. Bai yarda ya hallaka su ba, bai kuma yi watsi da su ba har wa yau.


Kamar yadda nisan sararin sama yake bisa kan duniya, Haka kuma girman ƙaunarsa yake ga waɗanda suke tsoronsa.


Fushinsa ba ya daɗewa, Alherinsa kuwa har matuƙa ne. Mai yiwuwa ne yă zama ana kuka da dare, Amma a yi murna da safe.


Amma Allah ya yi wa jama'arsa jinƙai, Ya gafarta zunubansu, Bai hallaka su ba. Sau da yawa yakan kanne fushinsa, Ya dakatar da hasalarsa.


Ana nan, a kwana a tashi, sai Sarkin Masar ya rasu. Jama'ar Isra'ila suka yi nishi, suka yi kuka kuma saboda bautarsu, kukansu na neman gudunmawa ya kai gun Allah.


Ubangiji kuwa ya ce, “Na ga wahalar jama'ata waɗanda suke a Masar, na kuma ji kukansu da suke yi a kan shugabanninsu. Na san wahalarsu,


Ubangiji ya hukunta jama'arsa da ya sa aka kai su baƙuwar ƙasa. Ya sa iskar gabas mai ƙarfin gaske ta tafi da su.


“A ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke, Amma da ƙauna mai zurfi zan sāke karɓarki.


Ashe, Ifraimu ba ƙaunataccen ɗana ba ne? Ashe, shi ba ɗan gaban goshina ba ne? A duk lokacin da na ambace shi a kan muguntarsa Nakan tuna da shi da ƙauna. Saboda na ƙwallafa zuciyata a kansa, Hakika zan yi masa jinƙai, ni Ubangiji na faɗa.


Ƙaunar Ubangiji ba ta ƙarewa, Haka kuma jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.


“Ƙaƙa zan iya rabuwa da ke, ya Ifraimu? Ƙaƙa zan miƙa ki, ya Isra'ila? Ƙaƙa zan maishe ki kamar Adma? Ƙaƙa zan yi da ke kamar Zeboyim? Zuciyata tana motsawa a cikina, Juyayina ya huru.


Ni Ubangiji na ce, “Ko da yake suna da ƙarfi, suna kuma da yawa, Za a datse su, su ƙare. Ko da yake na wahalar da kai, Ba zan ƙara wahalar da kai ba.


Sai ya tashi, ya taho wurin ubansa. Amma tun yana daga nesa, sai ubansa ya hango shi, tausayi ya kama shi, ya yiwo gudu, ya rungume shi, ya yi ta sumbatarsa.


Sa'an nan suka zubar da gumakan da suke wurinsu, suka yi wa Ubangiji sujada. Shi kuwa ya damu saboda azabar da Isra'ilawa suke sha.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan