27 Yana da kyau mutum ya hori kansa tun yana yaro.
27 Yana da kyau mutum yă sha wuya tun yana yaro.
Horon da aka yi mini ya yi kyau, Domin ya sa na koyi umarnanka.
Ka koya mana mu sani ranmu na ɗan lokaci ne, Domin mu zama masu hikima.
Ya Ubangiji, mai farin ciki ne mutumin da kake koya wa, Mutumin da kake koya masa shari'arka.
Ka tuna da Mahaliccinka a kwanakin samartakarka kafin mugayen kwanaki da shekaru su zo, da za ka ce, “Ba na jin daɗinsu.”
Yana da kyau a jira ceton Ubangiji da natsuwa,
Bari ya zauna a kaɗaice, ya yi shiru Sa'ad da yake da damuwa.