Ba ku za ku yi wannan yaƙi ba, ku dai, ku jā dāga, ku tsaya kurum ku ga nasarar da Ubangiji zai ciwo muku, ya Yahuza da Urushalima. Kada ku ji tsoro ko ku razana, gobe ku fita ku tsaya gāba da su, gama Ubangiji yana tare da ku.’ ”
Ka natsu a gaban Ubangiji, Ka yi haƙuri, ka jira shi, Kada ka damu da waɗanda suke da dukiya, Ko su da suka yi nasara da aikata mugayen shirye-shiryensu.
Sai Musa ya ce wa jama'a, “Kada ku tsorata, ku tsaya cik, ku ga ceton Ubangiji, wanda zai yi muku yau, gama Masarawan nan da kuke gani yau, ba za ku ƙara ganinsu ba faufau.
Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya ce wa jama'a, “Ku komo gare ni a natse, ku dogara gare ni. Sa'an nan za ku zama ƙarfafa ku zauna lafiya.” Amma ba ku yarda ba!
Faɗa masa ya zauna da shiri, ya natsu, kada ya ji tsoro ko ya damu. Fushin sarki Rezin da Suriyawansa da na sarki Feka ba wani abu mai hatsari ba ne, bai fi hayaƙin 'yan ƙirare biyu da suke cin wuta ba.
A cikin gumakan al'ummai akwai mai iya sa a yi ruwa? Sammai kuma su yi yayyafi? Ashe, ba kai ne ba, ya Ubangiji Allahnmu? Domin haka a gare ka muke sa zuciya, Gama kai ne mai yin waɗannan abubuwa duka.”
Gama har yanzu wahayin yana jiran lokacinsa, Yana gaggautawa zuwa cikarsa, Ba zai zama ƙarya ba. Ka jira shi, ko da ka ga kamar yana jinkiri, Hakika zai zo, ba zai makara ba.