Ya ce mini in tafi wajen arewa in yi shela in ce, “Ki komo ya Isra'ila, marar aminci, Ni Ubangiji, na faɗa. Domin ni mai jinƙai ne, Ba zan yi fushi da ke ba. Ba zan yi fushi da ke har abada ba, Ni, Ubangiji na faɗa.
Gama ina tare da kai don in cece ka, Zan hallaka dukan al'ummai sarai, Inda na warwatsa ku. Amma ku ba zan hallaka ku ba, Zan hore ku da adalci, Ba yadda za a yi in ƙyale ku ba hukunci, Ni Ubangiji na faɗa.”
Ashe, Ifraimu ba ƙaunataccen ɗana ba ne? Ashe, shi ba ɗan gaban goshina ba ne? A duk lokacin da na ambace shi a kan muguntarsa Nakan tuna da shi da ƙauna. Saboda na ƙwallafa zuciyata a kansa, Hakika zan yi masa jinƙai, ni Ubangiji na faɗa.