21 Da na tuna da wannan, sai na sa zuciya ga gaba.
21 Duk da haka na tuna da wannan na kuma sa bege ga nan gaba.
Na tafke, ya Ubangiji, jira nake ka cece ni, Na dogara ga maganarka.
Ya Isra'ila, ki dogara ga Ubangiji, Saboda ƙaunarsa madawwamiya ce, A koyaushe yana da nufin yin gafara.
Ƙaunar Ubangiji ba ta ƙarewa, Haka kuma jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.
Gama har yanzu wahayin yana jiran lokacinsa, Yana gaggautawa zuwa cikarsa, Ba zai zama ƙarya ba. Ka jira shi, ko da ka ga kamar yana jinkiri, Hakika zai zo, ba zai makara ba.