20 Kullum raina yana tunanin azabaina, Raina kuwa ya karai.
20 Na tuna su sosai, sai kuma na ji ba daɗi a raina.
Sa'ad da na tuna da abin da ya same ni, Sai jikina ya yi suwu, in yi ta makyarkyata ina rawar jiki.
Yakan ba makafi ganin gari. Yakan ɗaukaka waɗanda aka wulakanta. Yana ƙaunar jama'arsa, adalai.
Me ya sa ni ɓacin rai haka? Me ya sa ni damuwa? Zan dogara ga Allah. Har yanzu ma zan yabe shi, Mai Cetona, Allahna.
Me ya sa nake baƙin ciki? Me ya sa nake damuwa? Zan dogara ga Allah, Zan ƙara yabonsa, Mai Cetona, Allahna.
Mun fāɗi, an turmushe mu a ƙasa, An bar mu kwance cikin ƙura.
Sa'ad da nake alhini, ina cikin damuwa, Ka ta'azantar da ni, ka sa in yi murna.