Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 3:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Ka tuna da azabata, da galabaitata, Da ɗacin raina, da kumallon da nake fama da shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Na tuna da azabata da kuma sintiri, da na yi ta yi da ɗacin rai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 3:19
9 Iomraidhean Croise  

“Ya Allah, Allahnmu, da girma kake! Kai mai banrazana ne, cike da iko! Da aminci ka cika alkawaranka da ka alkawarta. Daga lokacin da Sarkin Assuriya ya danne mu, Har yanzu ma, wace wahala ce ba mu sha ba! Sarakunanmu, da shugabanninmu, da firistocinmu, Da annabawanmu, da kakanninmu, Da dukan sauran jama'arka sun sha wahala. Ka san irin wahalar da muka sha.


“Ka tuna, ya Ubangiji, raina iska ne kawai, Farin cikina ya riga ya ƙare.


Ya Ubangiji, kada ka manta da Dawuda Da dukan irin aikin da ya yi.


Ka tuna kwanakin mutum kaɗan ne, ya Ubangiji, Ka tuna yadda ka halicci mutane duka masu mutuwa ne!


Kada ka manta da yadda aka ci mutuncina, ni da nake bawanka, Da yadda na daure da dukan cin mutuncin da arna suka yi mini.


Mutanen Urushalima sun ce, “Don me muke zaune kawai? Bari mu tattaru, mu tafi cikin garuruwa masu garu, Mu mutu a can, Gama Ubangiji Allahnmu ya ƙaddara mana mutuwa, Ya ba mu ruwan dafi, Domin mun yi masa laifi.


Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, zan ciyar da mutanen nan da abinci mai ɗaci, in shayar da su da ruwan dafi.


Ya shayar da ni da ruwan ɗaci, Ya ƙosar da ni da abinci mai ɗaci.


Ya kewaye ni da yaƙi, Ya rufe ni da baƙin ciki mai tsanani da wahala.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan