Duwatsu da tuddai za su ragargaje, Amma ƙaunar da nake yi miki ba za ta ƙare ba sam. Zan cika alkawarina na salama har abada.” Haka Ubangiji ya faɗa, shi wanda yake ƙaunarki.
A kan dukan tsaunukan nan na hamada Masu hallakarwa sun zo, Gama takobin Ubangiji yana ta kisa Daga wannan iyakar ƙasa zuwa waccan, Ba mahalukin da yake da salama.
“Ka ƙi Yahuza ke nan ɗungum? Ranka kuma yana jin ƙyamar Sihiyona ne? Me ya sa ka buge mu, har da ba za mu iya warkewa ba? Mun zuba ido ga samun salama, amma ba wani abin alheri da ya zo. Mun kuma sa zuciya ga warkewa, amma sai ga razana.
Ubangiji kuma ya ce, “Kada ka shiga gidan da ake makoki, ko ka tafi inda ake baƙin ciki, kada ka yi baƙin ciki saboda su, gama na ɗauke salamata, da ƙaunata, da jinƙaina daga wurin jama'an nan.
“Ina kuka saboda waɗannan abubuwa, Hawaye suna zuba sharaf-sharaf daga idanuna. Gama mai ta'azantar da ni, Wanda zai sa in murmure yana nesa da ni. 'Ya'yana sun lalace, Gama maƙiyi ya yi nasara!”
Gama kafin waɗannan kwanaki, mutum da dabba ba su da abin yi. Ba kuma zaman lafiya ga mai fita da shiga saboda maƙiya, gama na sa kowane mutum ya ƙi ɗan'uwansa.