Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce a kan annabawa, “Ga shi, zan ciyar da su da abinci mai ɗaci, In shayar da su da ruwan dafi. Daga wurin annabawan Urushalima Rashin tsoron Allah ya fito ya mamaye dukan ƙasar.”
“Za ka kuma faɗa musu cewa, ‘In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ku sha, ku bugu, ku yi amai, ku fāɗi, kada kuma ku tashi saboda takobin da zan aiko muku.’