Zan sa musu masu hallakarwa huɗu, in ji Ubangiji, “da takobi don kisa, da karnuka don yayyagawa, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobin duniya don su cinye, su hallakar.
Domin haka zaki daga kurmi zai kashe su, Kyarkeci kuma daga hamada zai hallaka su. Damisa tana yi wa biranensu kwanto, Duk wanda ya fita daga cikinsu sai a yayyage shi, Domin laifofinsu sun yi yawa, Karkacewarsu babba ce.
“Ga abin da ya ce, ‘Dabba ta huɗu za ta zama mulki na huɗu a duniya, wanda zai bambanta da sauran mulkokin. Zai cinye duniya duka, ya ragargaje ta, ya tattake ta.
Mutane sun ce, “Zo, mu koma wurin Ubangiji, Gama shi ne ya yayyaga, Shi ne kuma zai warkar. Shi ne ya yi mana rauni, Shi ne kuma zai ɗaure raunin da maɗauri.
Ringin Yakubu kuma zai zamar wa al'umman duniya, Kamar yadda zaki yake a tsakanin namomin jeji, Kamar kuma yadda zaki yake a tsakanin garkunan tumaki, Wanda, sa'ad da ya ratsa, yakan tattaka, Ya yi kacakaca da su, Ba wanda zai cece su.
Har suka tula wa kansu ƙasa suna ta kuka, suna baƙin ciki, suna kururuwa, suna cewa, “Kaito! Kaiton babban birnin nan! Wanda duk masu jiragen ruwa a bahar suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa, A sa'a ɗaya ya hallaka.