Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 2:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Ƙofofinta sun nutse ƙasa, Ya lalatar, ya kakkarya ƙyamarenta, An kai sarkinta da mahukuntanta cikin al'ummai, Inda ba a bin dokokin annabawanta, Ba su kuma samun wahayi daga wurin Ubangiji.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Ƙofofinta sun nutse a cikin ƙasa; ya kakkarya ƙarafanta. Sarakunanta da ’ya’yan sarakunanta duk an kai su bauta cikin waɗansu ƙasashe, babu sauran doka, annabawa kuma ba su samun wahayi daga wurin Ubangiji.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 2:9
27 Iomraidhean Croise  

Aka kashe 'ya'yansa maza a idonsa, sa'an nan aka ƙwaƙule masa idanu, aka kuma ɗaure shi da sarƙa, aka kai shi Babila.


Isra'ila kuwa ta daɗe ba ta bin Allah na gaskiya, ba ta da firist mai koya mata, ba ta kuma bin shari'a.


Sai suka ce mini, “Waɗanda suka tsira, suka koma daga zaman talala, da suke can lardin, suna cikin wahala ƙwarai, suna kuma shan kunya. Garun Urushalima kuma ya rushe, ƙofofi sun ƙone.”


Ba sauran tsarkakan alamu, Ba sauran annabawan da suka ragu, Ba kuwa wanda ya san ƙarewar wannan.


Birnin ya zama kango, an farfashe ƙofofinsa.


Ubangiji kuwa ya ce mini, “Annabawa, annabcin ƙarya suka yi da sunana. Ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba, ban kuma yi magana da su ba. Annabcin da suke yi muku na wahayin ƙarya ne, dubar da suke yi marar amfani ce, tunaninsu ne kawai.


Ubangiji Mai Runduna ya ce wa mazaunan Urushalima, “Kada ku kasa kunne ga maganar annabawa, Gama sukan cika kunnuwanku da ƙarairayi. Suna faɗar ganin damarsu, Ba faɗar Ubangiji ba.


A rana ta tara ga watan huɗu, a shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Zadakiya, sai aka huda garun birnin.


Sai Kaldiyawa suka ƙone gidan sarki, da gidajen jama'a. Suka kuma rushe garun Urushalima.


Sojojin Babila sun daina yaƙi, suna zaune a cikin kagaransu. Ƙarfinsu ya ƙare, sun zama mata, An sa wa wuraren zamanta wuta, An karya ƙyamaren ƙofofin garinta.


Sojojin Kaldiyawa da suke tare da shugaban matsara, suka rushe dukan garun Urushalima.


Yahuza ta tafi bauta tana shan azaba, Da bauta mai tsanani. Tana zaune a tsakiyar sauran al'umma, Amma ba ta sami hutawa ba, Gama masu runtumarta sun ci mata, ba hanyar tsira.


Mutane suka yi ta yi musu ihu, Suna cewa, “Ku tafi, ku ƙazamai, Ku tafi, ku tafi, kada ku taɓa mu!” Don haka suka zama korarru, masu kai da kawowa. A cikin sauran al'umma mutane suna cewa, “Ba za su ƙara zama tare da mu ba.”


Shi wanda muke dogara gare shi, Wato zaɓaɓɓe na Ubangiji, ya auka cikin raminsu, Shi wanda muka ce, “A ƙarƙashin inuwarsa ne za mu zauna a cikin sauran al'umma.”


Zan yarɓa masa ragata in kama shi. Zan kai shi Babila, wato ƙasar Kaldiyawa, duk da haka ba zai gan ta ba, ko da yake zai rasu a can.


Zan kafa masa tarko in kama shi, sa'an nan in kai shi Babila inda zan yi masa shari'a saboda ya tayar mini.


Masifa a kan masifa, jita-jita a kan jita-jita. Suna neman wahayi daga wurin annabi, amma doka ta lalace a wurin firist, shawara kuma ta lalace a wurin dattawa.


Takobi zai ragargaje biranensu, Zai lalatar da sandunan ƙarafan ƙofofinsu, Zai cinye su domin muguwar shawararsu.


Gama mutanen Isra'ila za su zauna kwanaki da yawa ba sarki, ba shugaba, ba sadaka, ba al'amudi, ba falmaran, ba kan gida.


Zan ragargaje ƙyamaren ƙofofin birnin Dimashƙu, In kawar da masu sarautar Bet-eden da na kwarin Awen. Za a kwashe mutanen Suriya ganima zuwa ƙasar Kir.”


“Ubangiji zai bashe ku, ku da sarkin da kuka naɗa wa kanku ga wata al'ummar da ku da kakanninku ba ku sani ba. Can za ku bauta wa gumakan itace da na duwatsu.


Kamar yadda Ubangiji ya ji daɗi ya arzuta ku, ya riɓaɓɓanya ku, haka nan kuma zai ji daɗi ya lalatar da ku, ya hallaka ku. Za a fitar da ku daga ƙasar da za ku shiga, ku mallaka.


Saul kuwa ya yi tambaya ga Ubangiji, Ubangiji bai amsa masa ba, ko ta mafarkai, ko ta Urim, ko ta annabawa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan