Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 2:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Ubangiji ya wulakanta bagadensa, Ya kuma wofinta tsattsarkan Haikalinsa. Ya ba da garun fādodinta a hannun abokan gāba, Suka yi sowa a Haikalin Ubangiji Kamar a ranar idi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Ubangiji ya ƙi bagadensa ya kuma yi wofi da haikalinsa. Ya ba maƙiyinta fadodinta; suka yi sowa a cikin gidan Ubangiji kamar a ranar da ake yin biki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 2:7
31 Iomraidhean Croise  

Ya ƙone Haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan gidajen urushalima. Ya ƙone kowane babban gida.


Suka ƙone Haikalin Allah suke rushe garun Urushalima, suka ƙone dukan fādodinta, suka lalatar da dukan kayanta masu daraja.


Ka soke alkawarinka wanda ka yi wa bawanka, Ka jefar da kambinsa a cikin ƙazanta.


saboda haka kada ka yi fushi da mu ainun, ko ka riƙe da zunubanmu har abada, mu dai mutanenka ne, ka yi mana jinƙai.


“Ku faɗa wa Zadakiya, Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘Ga shi, zan juyo kayan yaƙin da suke hannunka waɗanda kake yaƙi da su gāba da Sarkin Babila, da sojojinsa, waɗanda suka kewaye garun birnin, zan kuwa tsiba kayan yaƙinka a tsakiyar birnin nan.


“Mika kuwa, mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya faɗa wa dukan mutanen Yahuza cewa, “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce, Za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za ta zama tsibin juji, Ƙwanƙolin dutsen Haikalin zai zama kurmi.’


Saboda haka zan mai da wannan Haikali kamar Shilo, in mai da wannan birni ya zama abin la'ana ga dukan al'umman duniya.”


Kaldiyawa da suke yaƙi da wannan birni za su zo, za su ƙone wannan birni da wuta ƙurmus, da gidaje waɗanda aka ƙona turare ga Ba'al a kan rufinsu. Aka kuma miƙa hadayu na sha ga gumaka, don su tsokane ni in yi fushi.


Sai Kaldiyawa suka ƙone gidan sarki, da gidajen jama'a. Suka kuma rushe garun Urushalima.


Na duba, sai na ga ƙasa mai dausayi ta zama hamada, An mai da dukan biranenta kangwaye A gaban Ubangiji saboda zafin fushinsa.


Gama Ubangiji ya ce, “Ƙasar duka za ta zama kufai, amma duk da haka, ba wannan ne zai zama ƙarshenta na har abada ba.


Ku ji, sun gudu sun tsere daga ƙasar Babila, Don su faɗa cikin Sihiyona, Sakayyar Ubangiji Allahnmu domin Haikalinsa.


Sai ya ƙone Haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan manyan gidajen da suke Urushalima.


Hanyoyin Sihiyona suna baƙin ciki Domin ba mai halartar ƙayyadaddun idodi. Dukan ƙofofinta sun zama kufai, Firistocinta suna nishi, Budurwanta kuma suna wahala, Ita kanta ma tana shan wuya ƙwarai.


Ubangiji ya duhunta Sihiyona saboda fushinsa! Daga Sama kuma ya jefar da darajar Isra'ila a ƙasa. Bai kuma tuna da matashin sawayensa ba A ranar fushinsa.


Ubangiji ya zama kamar maƙiyi, ya hallaka Isra'ila. Ya hallaka fādodinta duka, Ya mai da kagaranta kango. Ya aukar wa Yahuza da makoki da baƙin ciki mai yawa.


in faɗa wa mutanen Isra'ila, cewa Ubangiji Allah ya ce, ‘Zan ƙazantar da Haikalina, abin fariyarku, da abin da idanunku suke jin daɗin ganinsa, da abin faranta zuciyarku. 'Ya'yanku maza waɗanda kuka bari a baya, za a kashe su da takobi.


Zan kawo al'ummai masu muguntar gaske su mallaki gidajensu. Zan sa fariyar masu ƙarfi ta ƙare. Za a ƙazantar da masujadansu.


Zan sa biranenku su zama kangwaye, in mai da wuraren yin sujada kufai, ba zan shaƙi ƙanshin turarenku ba.


Duk da haka, sa'ad da suke a ƙasar maƙiyansu ba zan wulakanta su ba, ba kuwa zan ji ƙyamarsu, har da zan karya alkawarina da su ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu.


Saboda haka zan aukar da wuta a kan Yahuza Ta ƙone kagarar Urushalima.”


Saboda ku kuwa za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za ta zama tsibin kufai, Dutse inda Haikali yake zai zama kurmi.


Amma ya amsa musu ya ce, “Kun ga duk waɗannan ko? Hakika, ina gaya muku, ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan'uwansa ba a baje shi ba.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan